Babu wariyar launin fata a kwallon kafa-Blatter

blatter
Image caption Sepp Blatter

Shugaban hukumar kwallon duniya-Fifa Sepp Blatter ya ce kwallon kafa bata da matsala akan batun wariyar launin fata, inda yace idan aka samu matsala za a iya warware da ta hanyar gaisawa da hannu.

Hukumar kwallon Ingila wato FA a halin yanzu tana binciken John Terry na Chelsea da Luis Suarez na Liverpool akan batun kalaman wariyar launin fata.

Amma Blatter ya shaidawa gidan talabijin na CNN cewar" Babu wariyar launin fata, sai dai kawai kalamai ko kuma alamun da basu dace ba".

Yace "idan an samu hakan, za a iya warwarewa ta hanyar gaisawa".

Wannan kalaman na Blatter sun janyo suka daga wajen 'yan wasa kamarsu Rio Ferdinand na Manchester United.

Shima tsohon dan wasan Tottenham Hotspur Garth Crooks yace akwai gyara a kalaman Blatter.

Karin bayani