Shin ya kamata Blatter ya ajiye aikinsa?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Fifa, Sepp Blatter na fuskantar matsin lamba saboda kalamun wariyar launin fata.

Shugaban kungiyar kwarrarun 'yan kwallon kafa a Ingila,Gordon Taylor ya ce kamata ya yi, Shugaban Fifa Sepp Blatter ya ajiye aikinsa, saboda kalaman da ya yi akan wariyar launin fata.

Blatter dai ya ce ba'a samun matsalar wariyar launin fata a cikin filin wasa.

Taylor ya shaidawa BBC cewa,"Idan kuka ga yadda matsalar cin hanci ta dabaibaye Fifa, ina ganin wannan furucin nasa ya kara dagula komai".

"Ga kuma furucin da ya yi cewa 'yan luwadi da madugo ba za su je Qatar ba, a don haka lokaci ya yi da Shugaban Uefa Michel Platini ya karbi ragamar aiki."

Taylor dai yana maida martani ne, game da furucin da Blatter ya yi a wata hira da gidajen talibijin biyu inda ya ce babu matsalar wariyar launin fata ba a harkar kwallon kafa.

"Zan musanta hakan. Babu wariyar launin fata." In ji Blatter.

Kalaman na Blatter shine cece kuce na baya baya nan a kan Fifa, wadda Blatter mai shekarun haihuwa 75 ke jagoranta tun daga shekarar 1998.

'Takun saka tsakanin Blatter da Bin Hammam'

An dai dakatar da tsohon dan takarar neman kujerar Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya Mohamed Bin Hammam, daga duk wata harkar kwallon kafa a farko wannan shekara, bayan an same shi da laifin bada cin hanci, domin samun kuri'u.

Haka zalika an dakatarda mataimakin shugaban Fifa, Jack Warner akan batun zargin cin hanci da rashawa kafin daga bisani ya ajiye aikinsa.

A baya dai Blatter ya fuskanci matsin lamba, saboda ya ce Ingila ta wuce gona da irin bayan ta kwace mukamin kyaftin daga John Terry, sannan kuma akan kalaman da yi game da Cristiano Ronaldo, inda ya ce ana son a maida dan wasan bawa, bayan Manchester United tana jan kafa a lokacin da dan wasan ya nuna aniyar cewa yana son ya kama Real Madrid.

Har wa yau Blatter ya ce, kwallon mata zai inganta idan su ka fara sa guntayen wanduna masu dame jiki.

A ranar alhamis, Blatter ya yi amfani da shafinsa na Twitter, inda ya rubuta cewa; " Mun yi shirye shiryen hadin gwiwa domin wayar da kan jama'a a kan wariyar launin fata a kasar Afrika ta kudu. Fifa ta kafa tarihi wajen yaki da masu wariyar launin fata."

Mataimakin Shugaban Hukumar Fifa, a Burtaniya Jim Boyce, ya ce; "Na mamakin jin kalamun Blatter, amma nayi farin cikin cewa shi da da Fifa sun fito sunyi karin hake game da batun.

"Ya kamata kada ayi sakwa sakwa da harkar wariyar launin fata ko kadan, ko kuma kowani irin babanci da ake nunawa a wasa. Na san cewa mutane da dama a Fifa da kuma Uefa na aiki tukuru domin ganin an magance matsalar a harkar kwallon kafa."

Har wa yau Ministan wasanni Hugh Robertson da kuma Ministan wasanni a bangaren 'yan adawa a Burtaniy, Clive Efford, duk sun yi kira da Blatter ya auka daga kan kujerarshi.

Garth Crooks, Jakadan gangamin kungiyar yaki da wariyar launin fata mai suna 'Kick It Out' ya ce bai da ce a ce babu wariyar launin fata a harkar kwallon kafa ba.

"Idan ana so ayi Fifa matsin lamba, ba ta bangaren kasa kawai bane dolene abokan hulda kasuwancinsu su fuskanci matsin lamba, wannan ne kuma ya zai sa Hukumar ta gane kurenta."

Karin bayani