Ya kamata Blatter ya ajiye mukaminsa-Taylor

blatter Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sepp Blatter

Shugaban Kungiyar kwarrarun 'yan kwallon kafa a Ingila, Gordon Taylor ya ce kamata ya yi, Shugaban Fifa Sepp Blatter ya ajiye aikinsa, saboda kalaman da ya yi akan wariyar launin fata.

Blatter dai ya ce ba'a samun matsalar wariyar launin fata a cikin filin wasa.

Taylor ya shaidawa BBC cewa, "Idan kuka ga yadda matsalar cin hanci ta dabaibaiye Fifa, ina ganin wannan furucin nasa ya kara dagula komai".

"Ga kuma furucin da ya yi cewa 'yan madigo ba za su je Qatar ba; lokaci ya yi da Shugaban Uefa Michel Platini ya karbi ragamar aiki."

Taylor dai yana maida martani ne, game da furucin da Blatter ya yi a wasu hira da ya yi da gidajen talibijin biyu wanda ya ce bai yadda akwai matsalar wariyar launin fata ba a harkar kwallon kafa.

"Zan musanta hakan. Babu wariyar launin fata." In ji Blatter.

Kalaman na Blatter shine cece kuce na baya baya nan a kan Fifa, wadda Blatter mai shekarun haihuwa 75 ke jagoranci tun daga shekarar 1998.

An dai dakatar da tsohon dan takarar neman kujerar Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya Mohamed Bin Hammam, daga duk wata harkar kwallon kafa a farko wannan shekara, bayan an same shi da laifin bada cin hanci, domin samun kuri'u.

Haka zalikam shima an dakatar a mataimakin Shugaban Hukumar, Jack Warner shima wadda aka dakatar a yayinda ake binciken shi game da batun zargin cin hanci, shima ya ajiye aikinshi.

A baya dai Blatter ya fuskanci matsin lamba, saboda ya ce Ingila ta wuce gona da irin bayan ta kwace mukamin kyaftin daga John Terry, sannan kuma akan kalamun da yi game da Cristiano Ronaldo, inda ya ce ana son a maida dan wasan bawa, bayan Manchester United tana ja da baya a lokacin da dan wasan ya nuna aniyar cewa yana so ya kama Real Madrid.

Karin bayani