Esperance zata hadu da Al Sadd a Japan

Esperance Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Esperance ce ta lashe kofin Afrika

Zakaran kwallon Afrika Esperance za ta kara da Al Sadd ta nahiyar Asiya a wasan zagayen gabda na kusada karshe a gasar zakarun kulob na duniya da za ayi a Japan a wata mai zuwa.

Za a buga wasanne a ranar 11 ga watan Disamba a garin Toyota.

Duk kungiyar data samu nasara a wasa tsakanin Esperance da Al Sadd,zata hadu ne da Barcelona a zagayen kusada karshe.

Za a buga wasan zagayen kusada karshe a Yokohama a ranar 15 ga watan Disamba.

Shugaban Esperance Riadh Bennour ya ce baida tantama zasu taka rawar gani kamar wakilyar Afrika ta bara wato TP Mazembe ta Congo.

Da dama na saran ganin wasan karshe ya kasance tsakanin Santos da Barcelona.

Za a buga gasar daga ranar takwas zuwa 18 ga watan Disamba a Japan.

Karin bayani