Fellaini zai cigaba da taka leda a Everton

Marouane Fellaini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Marouane Fellaini

Dan wasan Everton Marouane Fellaini ya sabunta kwangilarsa a Goodison Park don cigaba da taka leda har zuwa 2016 a kulob din.

Fellaini mai shekaru 23 ya kasance babban dan kwallon kocinsa David Moyes tunda aka siyoshi akan fan miliyon goma sha biyar daga kungiyar Standard Liege ta Belgium a shekara ta 2008.

Shugaban Everton Robert Elstone ya bayyana cewar " Mun yi murnar samun Marouane na tsawo lokaci tare damu".

Fellaini ya zira kwallaye goma sha shida a wasanni 107 daya bugawa Everton kuma yana cikin tawagar data sha kashi a wasan karshe na kofin FA a shekara ta 2009.

Elstone ya kara da cewar "As everyone is aware these negotiations have been ongoing for some time but both parties remained positive that we would reach agreement."

Karin bayani