Tarihin kwallon Andre"Dede" Ayew na Ghana

Andre "Dede" Ayew Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Andre "Dede" Ayew

Ficen da Andre 'Dede' Ayew yayi a kwallon kafa ya zo tare da wasu 'yan kalubale.

Dan wasan mai shekaru 21 dan gida ne da suke yi fice a kwallon kafa saboda mahaifinsa Abedi Ayew Pele ya taba lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika sau uku, sannan kawunsa Kwame Ayew ya bugawa Ghana kwallo.

Ganin wannan tarihin, Dede ya nuna kansa a matsayin matashin dan wasa dake shirin fuskantar duk kalubalen dake gabansa.

Dede ya kasance kashin bayan nasarorin da Marseille ta samu a bana, inda ya taimakawa kulob din lashe gasar kwallon Faransa dana Super Cup.

Kwallayen ukun daya zira a ragar Lille sune suka baiwa kulob din nasara daci biyar da hudu a wasan kofin Super a watan Yuli.

A karshen kakar wasan data wuce, Dede ya ci kwallaye 11 a Marseille sannan kuma a kakar wasa ta bana yaci kwallaye hudu.

Sannan kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen samowa Ghana gurbin zuwa gasar kwallon kasashen Afrika da za ayi a badi.

Ya kuma haskaka matuka a tawagar Black Stars data kai zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin duniya da kuma gasar kwallon matasan duniya da Ghana ta lashe a shekara ta 2009.

Dede na cikin 'yan wasan da Claude Le Roy ya gayyata cikin tawagar Ghana a gasar kofin Afrika na 2008, inda aka yita sukar dan wasan saboda kasa zira kwallo.

Can a Marseille an taba bada aronsa zuwa Arles Avignon kafin ya nunawa kocinsa Didier Deschamps cewar ya iya murza leda.

Kawo yanzu dai a kakar wasa ta bana Dede Ayew ya nuna cewar dashi za aje, kuma a matsayinsa na dan shekaru 21 wanda ya bugawa kasarsa kwallo a wasanni 32, bisa dukkan alamu gaba zata fi baya kyau.