Liverpool ta doke Chelsea daci biyu da daya

Chelsea Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Johnson ne ya jikawa Chelsea gari

Glen Johnson yaci kwallon daya baiwa Liverpool nasara akan Chelsea a wasan gasar premier ta Ingila da suka buga a filin Stamford Bridge.

A kakar wasan data wuce ma Liverpool ta doke Chelsea gida da waje, kuma a yanzu ma kulob din ta Anfield ce ta samu galaba.

Maxi Rodriguez ne ya ciwa Liverpool kwallon farko a yayinda Daniel Sturridge wanda ya shigo bayan hutun rabin lokaci ya farkewa Chelsea.

Ana gabda tashi wasan sai Glen Johnson ya ciwa Liverpool kwallon daya bata nasara.

Wannan ne dai wasa na uku cikin guda hudu da aka samu galaba akan Chelsea a gasar premier ta Ingila.