Tarihin kwallon Gervinho na Ivory Coast

Gervinho Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Gervinho da kocinsa Arsene Wenger

Gervinho mai shekaru 24 ya lashe kofin farko a tarihinsa ne a bana, amma dai kawo yanzu yana kokarin gano bakin zaren a sabon kulob dinsa Arsenal.

Kafin ya koma gasar Premiership ta Ingila a watan Yuli, Gervinho ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar lashe kofina biyu da Lille ta yi a Faransa, inda ya zira kwallaye 18 a kakar wasan data wuce.

A karshen kakar wasan data wuce manyan kulob kamarsu Paris Saint Germain da kuma Atletico Madrid sun yi zawarcinsa kafin ya koma Arsenal akan kusan dala miliyon 17.

Yaci kwallaye biyu a mintuna 15 na farko da saka rigar Arsenal a wasan sada zumunci tsakaninsu da FC Koln.

Tun komawarsa Emirates, ana bashi damar taka leda inda yaci kwallaye biyu a wasanni takwas.

An haifi shi da sunan Gervais Yao Kouassi amma sai ya baiwa kanshi sunan 'yan Brazil 'Gervinho' tun lokacin yana bugawa Asec Mimosas.

Ya koma taka leda a Turai a shekara ta 2004 inda ya bugawa kungiyar Beveren ta Belgium kafin ya koma Faransa.

Da farko Gervinho ya bugawa Le Mans a Faransa daga bisani ya koma Lille a shekara ta 2009. A shekaru biyun da suka wuce, ya kasance gwarzon dan kwallon Ivory Coast amma kuma a halin yanzu magoya bayan Arsenal sun rarrabu akan mahimmancin siyoshi.