Beckham ya lashe gasa tare da L.A Galaxy

David Beckham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Beckham

David Beckham ya taimakawa LA Galaxy ta lashe gasar kwallon kafa a Amurka bayan nasarar da suka yi akan Houston Dynamo a wasan karshe daci daya me ban haushi.

Beckham mai shekaru 36 da Robbie Keane tare da Landon Donovan suka hadu suka baiwa kulob din kwallo daya daya bata nasara.

A wata mai zuwa ne kwangilar tsohon kyaftin din Ingila zata kare a Galaxy.

Akan batun makomarsa, Beckham yace"Ko zan tsaya ko zan tafi,na ji dadin shekaru biyar din dana yi".

Beckham wanda ya buga wasan karshen na mintuna casa'in duk da rauni a kafarsa, ya koma Galaxy ne daga Real Madrid a shekara ta 2007.

Magoya bayan Galaxy sun yita wakokin cewar"muna son Beckham", bayanda kulob din ya lashe kofi a karon farko tun shekara ta 2005.

Kwangilarsa zata kare a karshen watan Disamba kuma zai shiga cikin rangadin da kulob din zai yi a Indonesia da Philippines da kuma Australia wanda za a fara a mako mai zuwa.

Beckham ya lashe kofina gasar premier guda shida tare da Manchester United kuma ya bayyana cewar yanason ya kasance cikin tawagar da zata bugawa Ingila kwallo a gasar Olympics ta badi.

Karin bayani