Anelka zai bar Stamford Bridge a 2012

 Nicolas Anelka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nicolas Anelka

Dan wasan Chelsea, Nicolas Anelka ya amince zai bar Stamford Bridge idan kwangilarsa ta kare a shekara ta 2012.

Dan kwallon mai shekaru 32, kwangilarsa zata kare ne a karshen kakar wasa ta bana, kuma yanada damar sanya hannu a kwangila ta wani kulob a cikin sabuwar shekara.

Akwai wani batu a kwangilar Anelka dake nuna cewar dan wasan nada damar sabunta kwangilarsa ta karin shekara guda.

Ganin cewar kulob din bai bashi damar sabunta kwangilarsa ba, a yanzu Anelka ya yanke shawarar barin Chelsea a karshen kakar wasa ta bana.

Anelka ya bayyanawa jaridar 'The Times' ya ce "Ina son bugawa a nan, ina jin dadin bugawa da Didier Drogba, John Terry, Frank Lampard da kuma Florent Malouda".

Kulob da dama sun nuna sha'awa akan tsohon dan wasan Arsenal da Real Madrid, saboda dai kungiyar Shanghai Shenhua ta China ta nuna kwadayin sayenshi.

Har wa yau AC Milan da Anzhi Makhachkala ta Rasha da kuma wasu kulob a Amurka suna zawarcin Anelka.

Karin bayani