Manchester City na tsaka mai wuya - Mancini

mancini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce kulob dinsa nada dama kashi talatin cikin dari na tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar zakarun Turai bayan da suka sha kashi a wajen Napoli.

City ta sha kashi a Italiya daci biyu da daya a ranar Talata, kuma a yanzu tana bukatar ta doke Bayern Munich tare saran cewar Villarreal zata tashi canjaras a wasanta da Napoli, don ita City din ta tsallake zuwa zagaye na gaba.

Mancini yace"burinmu shine mu tsallake zuwa zagaye na biyu, amma a yanzu mun dogara ne akan wasu kulob din".

Ya kara da cewar"idan Villarreal ta zage damtse zamu samu gurbin amma kuma idan ta buga wasa yadda ta saba, to bamu da wata dama".

Edinson Cavani ne yaci wa Napoli kwallayenta biyu a yayinda Mario Balotelli ya farkewa City kwallo daya.

Karin bayani