Za mu farfado a wasanmu da Bayer Leverkusen

Andre Villas-Boas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya ce kulob dinsa zai shawo kan matsalolin da yake fuskanta a wasan da zai kara da Bayer Leverkusen na Zakarun Turai.

Kocin dan kasar Portugal na fuskantar matsin lamba bayan da aka doke kulob din a wasanni uku cikin hudu a Ingila.

Villas-Boas yace"Zamu iya canza sakamakon, munason mu nunawa jama'a cewar zasu iya samun kwarin gwiwa akanmu".

Villas-Boas na fuskantar matsala a wannan lokacin kuma ya kasance wanda ya takka mummunar rawa tun lokacin da Roman Abramovich ya sayi Chelsea a shekara ta 2003.

Kocin mai shekaru 34 ya ce baida wata damuwa akan makomar kulob din.

Sauran wasanni Zakarun Turai da za a buga:

*Zenit St Petersburg VS APOEL *BATE VS Viktoria Plze? *Valencia VS Genk *Olympique Marseille VS Olympiakos *Arsenal VS Borussia Dortmund *Shakhtar Donetsk VS Porto * AC Milan VS Barcelona

Karin bayani