Chelsea na tunanin komawa kwallo a Battersea

 Battersea.
Image caption Tashar samarda wuta a Battersea.

Chelsea na duba yiwuwar gina sabon filin wasa wanda zai kunshi mutane kusan dubu hamsin da biyar zuwa sittin a kusada tashar samarda lantarki na Battersea.

Kulob din dai bai yanke shawarar barin Stamford Bridge ba saboda kulob din na bukatar sayen filin Stamford bridge daga wajen magoya bayansa.

Amma kuma kulob din ya baiwa wani kamfanin zayyane-zayyane kwangilar fitar da wani tsarin sauya wajen filin wasan.

Kakakin Chelsea yace"A baya mun tattauna akan batun kusada tashar lantarki ta Battersea, amma dai bamu yanke shawara ba akai.

Akan wannan batun dai Chelsea ta nada Mike Hussey shugaban kamfanin Almacantar a matsayin wadanda zasu taimaka wajen ginin.

Akwai matsala akan filin tashar lantarki ta Battersea saboda masu filin na bukatar akalla fan dubu biyar da rabi don ginin.

An daina samarda lantarki daga tashar tun a shekarar 1983, amma kuma ana amfani da wajen don yin bukukuwa saboda a yanzu ma a can ake fafatawa a gasar ATP World Tour Finals.