Watakila ayi amfani da na'urar fasaha a 2012

goal
Image caption Kwallon da Lampard ya zira a ragar Jamus

Hukumar kwallon Ingila wato FA ta ce watakila ayi amfani da na'urar fasaha a gasar Premier ta Ingila a kakar wasa mai zuwa.

Sakatare Janar na FA din Alex Horne ya shaidawa BBC cewar akwai alamun sauya wasu dokokin kwallon kafa, idan har daya daga cikin na'urorin da aka gwada suka yi aiki.

Yace"Na'urar fasaha na tantance shigar kwallo a raga zai taimakawa kwallon kafa".

Ya kara da cewar "A cikin shekarunnan, alkalan wasan kan tafka kura-kurai".

A halin yanzu dai ana nazari akan wasu tsarin fasaha tara, kuma ana saran a watan Julin 2012 hukumar kwallon duniya wato Fifa zata yanke shawara akai.

Horne ya kuma bayyana cewar a kakar wasa ta 2012-2013 watakila sabuwar na'urar ta soma aiki.

Wannan kalaman nasa na nuna akan cewar watakila a yiwa dokokin kwallon kafa kafin a fara kakar wasa mai zuwa.

Karin bayani