Dortmond ta gargadi Arsenal akan Gotze

Mario Gotze Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mario Gotze

Kokarin Arsenal na sayen dan kwallon Jamus Mario Gotze ya gamu da cikas saboda Borussia Dortmund ta ce bana sayarwa bane.

Dan wasan tsakiya mai shekaru 19, Gotze ya buga wasan da Arsenal ta doke Dortmund daci biyu da daya a gasar zakarun Turai na ranar Laraba.

Arsenal na zawarcin Gotze wanda aka kimanta kudinsa akan fan miliyon talatin.

Amma darektan wasanni Michael Zorc ya ce "Ina da tabbas kashi 99 cikin 100 cewar Mario Gotze zai bugawa Borussia Dortmund a kakar wasa mai zuwa".

Gotze ya bugawa Jamus a wasanni 10 inda yaci kwallaye biyu kuma ya kasance dan kwallon da ake rububinsa a Turai saboda Manchester United da Bayern Munich duk suna sha'awarsa.

Amma kuma Zorc ya hakikance dan kwallon babu inda za shi.