Gwamnati na binciken lamarin Indomitable Lions

etoo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kyaftin din Kamaru Samuel Etoo

Fadar shugaban kasar Kamaru na bincike akan dalilan da suka janyon tawagar Indomitable Lions tayi yajin aiki a makon daya gabata.

Takaddama akan kudin alawus din 'yan wasa, ta janyo fasa buga wasan sada zumunci tsakanin Kamaru da Algeria.

Saboda takaddamar, ana saran Samuel Eto'o da Eyong Enoh su gurfana gaban kwamitin ladabtarwar hukumar kwallon Kamaru -Fecafoot a ranar Alhamis.

Amma kuma saboda shigar fadar shugaban kasa cikin lamarin, Fecafoot ta dakatar da binciken.

A baya dai an soki ministan wasanni da ilimin motsa jiki a Kamaru Michel Zoah bayan da aka fasa buga wasansu da Algeria a ranar 15 ga watan Nuwamba.

An samu rashin jituwa ne bayan da 'yan tawagar Indomitable Lions suka buga wasanni biyu tsakaninsu da Morocco da kuma Sudan a Marrekesh.

Bayan da aka ki baiwa 'yan wasan alawus dinsu, sai suka kauracewa wasansu da Algeria a matsayin matakin nuna rashin jin dadi.

Karin bayani