AC Milan na kokarin sayen Tevez daga City

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlos Tevez

BBC ta fahimci cewar AC Milan ta soma tattaunawa da wakilin Carlos Tevez don sayen dan kwallon Manchester City din a kasuwar musayar 'yan kwallo a watan Junairu.

Inter Milan da kuma Juventus suma sun nuna sha'awarsu akan Tevez, amma wakilin Tevez din Kia Joorabchian a ranar Alhamis ya gana da jami'an AC Milan.

City na kokarin sayen dan wasan mai shekaru 27 a matakin dun-dun-dun.

Ana saran Tevez zai bar City tun bayan da aka same shi da laifin saba ka'idar kwangilarsa a wasansu da Bayern Munich na zakarun Turai.

AC Milan na bukatar dan kwallon gaba don maye gurbin Antonio Cassano wanda ke jinya sakamakon tiyatar da aka yi masa a zuciya.

Akwai alamun cewar Manchester City ba zata sayarda Tevez ba har sai an biya kudin da take bukata.

Karin bayani