Togo ta nada Didier Six a matsayin koci

Togo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tawagar 'yan kwallon Togo

Hukumar kwallon Togo FTF ta sanarda kulla yarjejeniya da dan Faransa Didier Six a matsayin kocin tawagar 'yan kwallonta har zuwa gasar kofin duniya a 2014.

A watan Satumba ne hukumar kwallon ta Togo ta nemi wadanda ke sha'awar zamowa kocin 'yan kwallonta su mika takardunsu bayan tafiyar Thierry Froger.

Didier Six mai shekaru 57 ya jagoranci 'yan kwallon Togo bayanda a baya yaja ragamar Strasbourg.

Togo dai ta tsallake zuwa zagaye na gaba a wasanni share fagen neman gurbin zuwa gasar kwallon duniya da za ayi 2014, bayan da Togon ta doke Guinea Bissau daci biyu da daya.

A wadannan wasanni share fagen, Didier Six ne ya jagoranci Togo.