'Ba na bukatar taimako'- Villas Boas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya musanta cewa yana neman taimako wajen tafiyar da 'yan wasan sa.

Rahotanni dai na nuni da cewa tsohon kocin kungiyar Guus Hiddink, zai dawo kungiyar domin ya taimakawa Villas Boas.

Hiddink dai ya bar horon Turkiyya ne a makon daya gabata.

Amma Villas-Boas ya ce: "Ban yarda ba, ba ni kadai zan magance matsalar ba, zamu magance mastalar da muke fuskanta ne tare da wadanda suke aiki da ni da kuma 'yan wasana.

"Na yi imanin zan iya, kuma ina da kwarin gwiwa a kan 'yan wasa na."

An dai doke Chelsea a wasanni hudu cikin biyar da ta buga a baya baya nan.