Man City ta buga kunen doki da Liverpool

Man City Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Vincent Kompany ya saka kwallo a ragar Liverpool

Manchester City ta bada tazarar maki biyar a saman teburin gasar premier ta Ingila bayan ta tashi kunen doki wato daya da daya tsakaninta da Liverpool a wasan da suka buga a filin Anfield a ranar Lahadi.

Kyaftin din City Vincent Kompany ne ya ciwa kulob din kwallon mintuna goma sha biyar bayan an dawo hutun rabin lokaci bayan da David Silva ya buga masa kwallo daga kusurwa.

Sai dai bayan mintuna biyu sai Charlie Adams na Liverpool ya bugo kwallo da karfi sai dan Manchester City Joleon Lescott ta taba kwallon cikin ragarsu a yayinda ya sayarda golansu Joe Hart.

Man City sun koma wasa da 'yan kwallo goma a cikin fili bayan da alkalin wasa ya kori Mario Balotteli daga wasan.

Duka kungiyoyin biyu sun kai hari amma kwallon bata shiga raga ba.

Sakamakon wasan ya nuna cewar City na gaban Manchester United da maki biyar a saman tebur saboda United ta buga daya da daya tsakaninta da Newcastle.

Karin bayani