Alkalin wasa ne ya cutar damu-Ferguson

ferguson Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce baiwa Newcastle fenariti a wasan da suka tashi daya da daya a Old Trafford abun takaici ne.

Alkalin wasan Mike Jones ya bada fenariti a wasan baya mataimakinsa John Flynn ya daga tuta sakamakon kayarwar da Rio Ferdinand ya yiwa Ben Arfa.

Ferguson yace "Alkalin wasan ya dauka za ayi bugun kusurwa ne saboda baya kusada inda lamarin ya auku".

Sakamakon sauran karawar gasar premier:

*Stoke City 3 - 1 Blackburn Rovers *Bolton Wanderers 0 - 2 Everton *Chelsea 3 - 0 Wolverhampton Wanderers *Manchester United 1 - 1 Newcastle United *Norwich City 2 - 1 Queens Park Rangers *Sunderland 1 - 2 Wigan Athletic *West Bromwich Albion 1 - 3 Tottenham Hotspur *Arsenal 1 - 1 Fulham

Karin bayani