La Liga: Real ta haskaka, Barcelona ta fadi

real madrid Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan Real Madrid

Real Madrid ta cigaba da yin kaka gida a saman teburin gasar La Liga ta Spain bayan ta lallasa makwabciyarta Atletico daci hudu da daya, a yayinda Barcelona ta sha kashi a wajen Getafe.

Atletico ta fashe shekaru 12 bata samu galaba akan Real ba kuma a wasansu na ranar Asabar labarin bai canza ba, saboda Angel Di Maria da Gonzalo Higuain da kuma Cristiano Ronaldo sune suka ciwa Real kwallayenta.

A yanzu Real Madrid ta shiga gaban Barcelona da maki shida bayanda Getafe ta doke Barca daci daya me ban haushi.

Valencia wacce ke ta uku ta casa Rayo Vallecano daci biyu da daya.

Real Sociedad ta samu galaba akan Real Betis daci uku da biyu.

Karin bayani