Kocin Wales Gary Speed ya mutu a shekaru 42

Gary Speed Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Margayi Gary Speed

Kocin tawagar 'yan kwallon Wales Gary Speed ya mutu a shekaru arba'in da biyu.

Hukumar kwallon kasar Wales ce ta tabbatar da mutuwar a wata sanarwa data fitar.

Sanarwar ta ce"Muna juyayi tare da yin ta'aziya ga iyalansa, kuma muna fatar mutane zasu mutunta sirrin iyalansa a wannan mawuyacin halin".

Speed ya zama mai horadda 'yan kwallon Wales ne a watan Disambar 2010 kuma a farko wannan watan tawagarsa ta haskaka fiye da yadda aka zata.

Nasara daci hudu da daya a wasan sada zumunci tsakaninsu da Norway, itace nasara ta uku a jere da Speed ya jagoranci Wales.

Speed ya bugawa kasarsa Wales kwallo a wasanni 85 cikin shekaru 14.