'Yan kwallon Togo shida sun mutu a hadari

togo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taswirar Togo

Wasu manyan 'yan kwallon Togo shida sun mutu sakamakon faduwar motar dake dauke dasu sannan kuma ta kama da wuta.

Lamarin ya auku ne kilomita 160 daga arewacin Lome babban birnin kasar, a lokacin da tawagar Etoile Filante ke tafiya zasu je buga wasa.

Wasu 'yan kwallon da dama su kuma sun samu munannan raunuka.

Rahotanni sun nuna cewar hadarin ya auku ne sakamakon fashewar tayar motar dake dauke dasu.

Hadarin ya auke ne a ranar Asabar kusada birnin Atakpame.

Daya daga cikin wadanda suke tsira Mama Souleyman ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na AP cewar "bamu san yadda muka kubuta ba".

Kawo yanzu ba a bayyana sunayen wadanda suka mutu.

Shugaban kasar Faure Gnassingbe ya bada umurnin cewar akai wadanda suka jikkata zuwa asibitin sojoji.

Karin bayani