AC Milan na bukatar Tevez ne a matsayin aro

tevez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlos Tevez

AC Milan na sha'awar sayen dan kwallon Manchester City Carlos Tevez a watan Junairu amma kuma a matsayin aro, sai dai City din na bukatar musayar ta zamo ta dun-dun-dun, kamar yadda BBC ta fahimti.

Kawo yanzu dai AC Milan bata tuntubi City ba a hukumance, amma kuma shugaban Milan Adriano Galliani ya ce "Tevez? Bari mu gani akwai lokaci".

Galliani yace"Koma waye zai zo a watan Junairu sai dai a matsayin aro".

Milan na bukatar wanda zai maye gurbin Antonio Cassano saboda tiyatar da aka yi masa a zuciya.

Shugaban Inter Milan Massimo Moratti shima ya bayyana cewar "bari mu gani" a lokacin da aka tambayeshi ko suna da sha'awar sayen Tevez.

Karin bayani