Federer ya doke Tsonga a wasan ATP Finals

Roger Federer Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roger Federer

Roger Federer ya ce lashe gasar karshen shekara ta tennis sau shida a jere, babban abun murna ce gareshi a tarihinsa.

Federer ya doke Jo-Wilfried Tsonga a wasan na ATP World Tour Finals.

Yace"nayi matukar murna saboda nasara ce ta musamman a tarihin wasa na".

Federer ya lashe gasa a Basel da Paris kafin ya kwashe komai a London.

Babu wanda ya samu nasara akansa tun bayan gasar US Open a watan Satumba wato kenan kawo yanzu ya samu galaba a wasanni 17 a yayinda za a shiga shekara ta 2012.

Tsonga ya yi kokarin zamowa dan kasar Faransa na farko da zai lashe gasar, amma duka doke shi da akayi, ya nuna cewar zai iya kalubalantar manyan kamarsu Novak Djokovic, Rafael Nadal da kuma Andy Murray a shekara ta 2012.