Blackburn sun fid da rai da Carling Cup

Steve Kean Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blackburn sun buga wasanni biyar ba su ci ko daya ba

Kocin Blackburn Rovers, Steve Kean, ya tabbatar da cewa tun kafin karawarsu da Cardiff a wasan gab da na kusa da na karshe ya sarayar da damar kulob din nasa.

Kulob din Kean din ne dai a kasan tebur a gasar Premier League; bayan kashin da suka sha da ci biyu kuma cewa ya yi: "mun taka wani mataki da dole mu fitar da rai da samun damar kaiwa ga wasan karshe".

Ya kuma kara da cewa, "muna da wasannin da za mu kara da kungiyoyin da ke kusa da mu a tebur, saboda haka wajibi ne mu dauki wadannan wasannin tamkar wasan karshe na cin kofi".

A wasansu da Cardiff din dai har sau biyar Kean ya yi canji saboda kada ya jefa 'yan wasansa na baya uku--Christopher Samba, da Martin Olsson, da kuma Michel Salgado, wadanda da ma ke fama da rauni--cikin hadari.

"Mun yi haka ne saboda mu tabbatar da cewa wadannan 'yan wasan uku a shirye suke don wasan mu na ranar Asabar da Swansea", in ji Kean.