Dynamos za ta buga gasar zakarun Afrika

Image caption Kungiyar Dynamos ta kasar Zimbabwe

Kungiyar Dynamos ta kasar Zimbabwe ta ce za ta buga gasar zakarun Afrika da za a yi a badi, duk da matsalolin kudi da ta ke fuskanta.

Kungiyar dai ce ta zama ta biyu a gasar da aka shirya a shekarar 1998, sannan kuma ta buga wasan kusa da na karshe a shekarar 2008.

A bana dai kungiyar ce ta lashe gasar Premier a Zimbabwe a karo na goma sha tara.

A yanzu haka dai, kungiyar na fuskantar matsaloli, amma za ta yi shiga gasar zakarun Afrika, idan har ta buga gasar cin kofin Confederation.

Har wa yau, kungiyar ta lashe gasar kofin Mbada Diamonds, inda za ta samu kyautar dalan Amurka miliyan daya.

Sannan saboda shiga gasar cin kofin Confederation da kungiyar za ta yi, za ta samu tallafin dalan Amurka dubu dari da hamsin.