Trapattoni ya kula sabuwar yarjejeniya da Ireland

Hakkin mallakar hoto inpho
Image caption Giovanni Trapattoni

Kocin tawagar kwallon kafa na Jamhuriyar Ireland, Giovanni Trapattoni ya kulla sabuwar yarjejeniya da kasar inda zai jagoranci kasar zuwa wasanni share fage na gasar cin kofin duniya da za'a a shirya a shekarar 2014.

Kocin, mai shekarun haihuwa 72, tare da mataimakansa Marco Tardelli da Fausto Rossi sun taimakawa Ireland tsallakewa domin taka leda a gasar cin kofin Turai ta shekarar 2012.

Trapattoni ya ce: "Wannan wata babbar dama ce aka bani, kuma ina farin ciki zan ci gaba da aiki da tawagar kwallon kafan kasar.

"Ni da Marco muna da kwarin gwiwa a kan ayyukan da mu ke yi na inganta tawagar kwallon kasar Ireland."