Blackburn na bayana dari bisa dari -Kean

Steve Kean Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Blackburn Rovers, Steve Kean

Kocin Blackburn, Steve Kean, ya ce masu kulob din suna mara masa baya dari bisa dari, duk da cewa kulob din bai tabuka abin a-zo-a-gani ba a gasar Premier League.

Rovers din ne dai a kasan tebur, kasancewar suna da maki bakwai ne kawai daga wasanni goma sha uku; tuni ma wadansu magoya bayan kulob din suka yi zanga-zanga suna neman a kori kocin.

A cewar Kean, masu kulob din "suna goyon bayan duk abin da muke kokarin aiwatarwa".

Kocin dai ya fuskanci matsalar raunin manyan 'yan wasansa irin su Ryan Nelsen, da Martin Olsson, da Michel Salgado da Chris Samba a 'yan makwannin nan.

Kean ya ce ko da ya ke masu kulob din suna nuna damuwa da halin da ake ciki, suna tausayawa.

"Mun yi wata tattaunawa da daya daga cikin daraktocin kulob din; kuma ranar Litinin za mu gana da hukumar daraktocin don tattauna batun sayen 'yan wasa", in ji Kean, wanda ya yi shakulatin bangaro da kalaman da aka ruwaito cewa ya furta wadanda ke nuna kamar da gangan ya bari kulob din ya sha kashi a wasan gab da na kusa da na karshen na gasar Carling Cup.