Mancini ya gargadi Mario Balotelli

Roberto Mancini Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kocin Manchester City, Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya gargadi dan wasansa, Mario Balotelli, ya kiyayi abokan karawarsa wadanda ke son a kore shi daga filin wasa.

Mancini ya zargi 'yan wasan Liverpool da tunzura dan wasan lokacin da aka ba shi jan kati - jan katinsa na uku a watanni shida tun bayan zuwansa City - a wasansu na ranar Lahadi wanda suka yi kunne doki.

"Ya kamata Mario ya mai da hankali ya kuma bude ido sosai", in ji Mancini.

Kocin ya kuma kara da cewa, "Ni ba abin da zan iya yi; shi ne ya ke cikin filin. Don haka ya kamata ya mai da hankali ya kuma tattara tunaninsa a kan wasan kwallo kawai".

An dai baiwa Balotelli kati mai launin rawaya na biyu ne bayan minti goma sha takwas da shigarsa wasan a filin wasa na Anfield bayan hutun rabin lokaci saboda gaba-da-gaban da suka yi da Martin Skrtel a minti na tamanin da uku na wasan.

Mancini ya kuma ce da Balotelli ya buga a mintin ashirin na karshen wasan da City sun yi nasara.