Messi, Ronaldo, Xavi: Waye zakaran duniya?

Lionel Messi da Xavi Hernandez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan Barcelona, Lionel Messi da Xavi Hernandez

An ware sunayen Lionel Messi, da Cristiano Ronaldo, da kuma Xavi don ba daya daga cikinsu kyautar zakaran kwallon kafa na duniya.

Dan shekaru 24, Messi ne ya ci kyautar a shekarun 2009 da 2010 bayan ya ci kwallaye 53 a dukkan gasannin da ya buga a kakar wasa ta bara.

Da dama daga cikin hare-haren da ya kai dai ya kai su ne da taimakon Xavi, mai shekaru 31, wanda suke kulob daya.

Shi ma Ronaldo, mai shekaru 26 da haihuwa, ya ciwa Real Madrid kwallaye 53, yayin da suka kammala kakar a matsayi na biyu Barcelona kuma suka casa su a wasan kusa da na karshe na Champions League.