An daure tsohon dan wasan Manchester United

Ronnie Wallwork
Image caption Tsohon dan wasan Manchester United Ronnie Wallwork ya amsa laifinsa

Kotu ta yankewa wani tsohon dan wasan Manchester United wanda aka samu yana kwakkwance motocin sata hukuncin daurin watanni goma sha biyar a gidan kaso.

Ronnie Wallwork, mai shekaru 34 a duniya, ya amsa laifin da aka tuhume shi da shi na karbar kayan sata.

'Yan sanda ne dai suka yi kicibis da Wallwork yayin da suke bincike a kan wani fashi da aka yi wanda ba shi da alaka da tuhumar da ake yi masa.

Alkalin Kotun Preston ya ce bai gamsu da bukatar lauyar da ke kare Wallwork ba, cewa a yiwa tsohon dan wasan daurin talala.

Alkali Simon Newell ya shaidawa dan wasan wanda ya taba bugawa kungiyar kwallon kafa ta Ingila 'yan kasa da shekaru ashirin cewa: "kayan da aka sace kaya ne masu tsada matuka, kuma a ganina an yi amfani da kwarewa da dabara wajen sace su.

"Kuma a zahiri an sace su ne da nufin sayar da su a kasuwar bayan fage; kai kuma ka taimaka wajen aikata haka".

Bincike ya nuna cewa Wallwork ya sayar da injin din wata mota kirar Volkswagen Touran da kuma sassan BMW 318i a kasuwar intanet ta eBay, an kuma gan shi ya shiga da wata Mazda Furano garejin da yake kwakkwance motocin kwana uku bayan sace ta a wajen wani mai sayar da motoci.

An kiyasta motoci ukun da aka alakanta da shi sun tashi jumlar kudi fam dubu arba'in da uku.

Lauyar Wallwork, Rachel Woods, ta ce "shaidan ya yi nasarar rinjayar tsohon dan wasan ne a lokacin da ya fada cikin matsanancin halin rashin kudi".

A cewarta, Wallwork dan wasan kwallo ne mai tashe kafin sana'arsa ta kwallo ta zo karshe ba-girma-ba-arziki bayan wani hari da aka kai masa shekaru biyar da suka gabata.

Ta kara da cewa wanda ta ke karewar, bayan ya kusa rasa ransa lokacin harin, ya sha wahalar neman hanyar da zai bi don sake gina rayuwarsa.

Wallwork dai ya tafka mummunar asara a wadansu harkokin kasuwanci wadanda suka durkushe kafin ya bude garejin da aka kama shi yana sarrafa motocin sata.

Wallwork ya taba samun lambar yabo ta Premier League a shekarar 2001, amma a shekarar da ta biyo baya Manchester United ta baiwa West Bromwich Albion shi ba tare da ta karbi ko kwabo ba.

Shi ne kuma dan wasan West Brom mafi hazaka a kakar wasanni ta 2004 zuwa 2005.

Bayan ya yi wasa na dan lokaci ga Bradford City, da Barnsley, da kuma Huddersfield Town, ya koma Sheffield Wednesday a 2008, amma wasanni bakwai kawai ya buga musu.

Karin bayani