'A baiwa Villas-Boas lokaci' - Grant

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tsohon Kocin Chelsea, Avram Grant

Tsohon kocin Chelsea, Avram Grant ya bukaci kungiyar da kada ta sallami kocinta Andre Villas-Boas.

Villas Boas, mai shekarun haihuwa 34 na fuskantar matsin lamba, saboda an doke ta a wasanni uku cikin biyar da ta buga a jere a gasar ta Premier.

A yanzu haka maki tara ne ke tsakanin Chelsea wadda take ta shida a tebur da mai jagoranci a gasar Manchester City.

Amma Grant ya shaidawa BBC cewa: "Suna fuskantar kalubale, amma ya kamata su nunawa kocin goyon baya.

"Basa samu sakamako masu kyau, amma ya kamata su nunawa kocin goyon baya."

Grant, wanda Chelsea ta sallama, duk da cewa ya kaita wasan karshe a gasar zakarun Turai, da kuma ta biyu a gasar Premier a shekarar 2008, ya ce; "Ya kamata su ba sabon kocin duk goyon bayan da yake bukata.

"Kocin matashi ne ya kamata a bashi lokaci, domin sabbin kalubale ne yake fuskanta."

Villas-Boas dai ya nuna kwarin gwiwa zai dawo da kungiyar kan ganniyar ta.