'Mun fita a Turai' - Redknapp

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Tottenham, Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce yana sa ran za'a fidda kungiyarsa a gasar Europa, a wasan karshe da kungiyar za ta buga a rukunin da take nan da makwanni biyu.

PAOK dai ta doke Spurs ne da ci 2-1, a gidan Spurs a wasan da kungiyoyin biyu su ka buga a daren Laraba.

A yanzu haka dai, sai an samu wasu sakamakon a sauran wasanni a rukunin da Spurs take kafin ta iya tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

"Gaskiya ban ji dadin abun da ya faru ba, saboda ba zamu samu damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba ba." In ji Redknapp.

"Na so mu ci gaba a gasar amma hakan ba zai yiwu ba."

Ya kara da cewa: "Da kamar wuya mu kara gaba, abokan karawarmu sun taka rawar gani."