Sierra Leone na fuskantar dakatarwa

Hakkin mallakar hoto Getty

Kasar Sierra Leone na fuskantar dakatarwa daga harkokin kwallo kafa, saboda wata takkadama da ta taso tsakanin Hukumar kwallon kasar da gwamnatin kasar.

Ma'ikatar wasanni ta kasar dai ta dage gasar kwallon kafa a makon da ya gabata, saboda wata takkadamar da aka yi a wani taro tsakaninta da Hukumar kwallon kasar.

Hukumar Fifa dai ta yi barazanar daukar mataki a kan batun.

Tuni dai Ministan wasanni a kasar Paul Kamara ya dage dakatarwar da ya yiwa gasar, amma Hukumar kwallon kafa a kasar har yanzu na neman Fifa da ta dauki mataki a kan batun.

Hukumar kwallon kasar na neman ma'ikatar wasanni a kasar da ta yi mata alkawarin cewa ba za ta kara tsoma baki a kan harkokin ta ba.

Amma ma'ikatar wasanni ta ce kungiyoyi ne su ka amince da a dakatar da fara gasar.