Watakila Hernandez ba zai buga wasa ba - in ji Ferguson

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Javier Hernandez

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya ce watakila dan wasan gaba na kulob din, Javier Hernandez, ya kwashe kusan makonni hudu ba ya taka leda saboda raunin da ya samu a gwiwarsa lokacin da ya fadi a wasan United da Aston Villa.

Manchester United dai ta yi galaba akan Aston Villa da ci daya mai ban haushi a karawar da suka yi.

Sir Alex ya ce kulob din na fuskantar kalubale saboda faman da wasu 'yan wasan ke yi da raunuka a wannan lokaci.

Sai dai ya ce hakan ba zai razana su ba saboda kulob din na da kwararrun 'yan wasa.

Yanzu dai Hernandez zai bi sahun 'yan wasan kulob din da ba za su buga wasa a nan kusa ba kamar su Dimitar Berbatov da Michael Owen, wadanda basu buga wasan da kulob din ya yi a Villa Park ba, duk da ya ke Sir Ferguson ya ce sakamakon wasan ya yi masa dadi.