Tsohon dan wasan Brazil Socrates ya mutu

Image caption Socrates

Tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Brazil, Socrates, ya rasu yana da shekaru hamsin da bakwai a duniya.

Socrates, wanda shi ne ya jagoranci 'yan wasan kwallon kafar kasar, a lokaci da aka yi gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 1979 da shekarar 1982, ya mutu ne ranar Lahadi sakamakon matsanancin ciwon cikin da ya yi fama da shi.

Kafin mutuwar tasa dai, Socrates ya yi suna wajen kwankwadar barasa.

Ko da a shekarun da yake tashe, ya sha cewa barasa na taka rawa sosai a rayuwarsa, amma ya kara da cewa bata hana shi buga wasa kamar yadda ya kamata.

Matarsa dai ta ce Socrates ya yi fama da ciwon ciki ne sakamakon gubar da ya ci a abinci, kuma an garzaya da shi asibitin Abert Einstein da ke babban birnin kasar, Sao Paulo ranar Juma'a inda ya ce ga-garinku nan.