McIlroy ya fi Tiger Woods kwarewa —Donald

Luke Donald da Rory McIlroy Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luke Donald da Rory McIlroy

Zakaran kwallon golf na duniya, Luke Donald, ya ce ya yi amanna Rory McIlroy ya fi Tiger Woods kwarewa.

A cewar Donald, wanda zai kara da McIlroy a zagaye na farko na Gasar Duniya a Dubai ranar Alhamis: "In dai batu na kwarewa ne, to ina ganin Rory ya fi. Ina ganin Tiger yana aiki tukuru kodayaushe kuma yana da nutsuwa sosai".

In dai Donald ya zo na tara ko ma ya fi haka, to zai yi nasara a gasar ta Dubai, sannan kuma zai zama kan gaba a Turai da Amurka.

Donald ya ce bai yi mamaki ba da McIlroya ya lashe gasar Hong Kong Open ranar Lahadin da ta gabata, al'amarin da ya karfafa masa fatan lashe kyautar dala miliyan da rabi ta gasar ta Dubai.

Donald ya shige gaban 'yan kwallon golf na duniya ne ta hanyar dagewa, inda ya a goma sha tara cikin gasannin da ya shiga guda arba'in da biyar ya ke kasancewa a cikin 'yan wasa goma na farko yayin da ya yi na farko a hudu daga cikinsu.