Villas-Boas ya mai da martani ga masu suka

Andre Villas-Boas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Chelsea Andre Villas-Boas

Andre Villas-Boas ya ce Chelsea ta baiwa masu suka a kanta kunya da ta kai matakin kifa-daya-kwala a gasar cin kofin zakarun Turai bayan ta casa Valencia.

Kocin na Chelsea, wanda ke magana bayan nasarar kulob din da ci uku, ya yi ikirarin cewa 'yan wasansa na fama da danniya.

"'Yan wasana sun cancanci a mutunta su, amma ba samun hakan", in ji Villas-Boas, wanda ya kara da cewa "mutane da matsin lamba daban-daban sun sa mu a gaba; don haka wannan nasara ta kunyata kowa".

Nasarar da Chelsea ta yi a kan Valencia dai ita ce nasarar su ta biyar a wasanni goma sha dayan da suka buga na baya-bayan nan; sai dai kuma za ta ba su damar darewa saman Rukunin E bayan sun sha gaban Bayer Leverkusen na Jamus.

Villas-Boas ya kuma yi amfani da damar don kushe yadda kafofin yada labarai ke bayar da labarin kulob din.

A ganinsa Manchester City ba sa fuskantar irin matsin lambar da Chelsea ke sha, duk da cewa akwai yiwuwar za a fitar da su [Manchester City] daga gasar cin kofin zakarun Turai saboda kashin da suka sha a hannun Napoli.

A cewar Villas-Boas, "Bayar da labarin cewa Chelsea ta yi nasara kuma ta zama ta farko da ta kai matakin kifa-daya-kwala abin takaici ne a wurinku [kafofin yada labarai]".