Judy ta zama shugabar kungiyar Tennis

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu 'yan kwallon Tennis

Hukumar kwallon Tennis ta Burtaniya ta zabi Judy Murray a matsayin wacce za ta jagoranci bangaren mata na kungiyar Tennis ta kasar.

Kungiyar ce dai za ta fafata da Isra'ila a gasar kwallon Tennis wadda za a gudanar daga ranar daya zuwa hudu ga watan Fabrairun badi.

Misis Murray ta amince da mukamin inda ta ce hakan wata dama ce da aka ba ta don yi wa kasarta hidima.

Tun a watan Yuni babu shugaba a kungiyar kwallon Tennis ta Burtaniya, bayan da shugabanta, Nigel Sears, ya sauka daga shugabancin.