Anelka ya amince ya koma China

Image caption Anelka

Jami'ai a kulob din League na China, Shanghai Shenhua, sun ce dan wasan Chelsea, Nicholas Anelka, ya amince ya koma kulab din bayan sun tattauna da shi.

Da ma dai wakilan Anelkan sun tattauna sau da dama da na kulob din domin yiwuwar komawarsa cikin makonni uku masu zuwa.

Kakakin kulab din, Ma Yue, bai bayyyana cikakken bayani game da farashin da suka sayi dan wasan ba, sai dai ya ce Anelka :'' zai fara bugawa kulab din wasa a watan Janairu, idan aka gama tattauna wa game da kwangilar da zai sanya wa hannu''.

Ana sa ran kulab din zai kuma sayi tsohon dan wasan Faransa, Jean Tigana, domin ya kasance kocin kulab din.

Chelsea ta sayi Anelka a shekarar 2008 akan fan miliyan sha biyar, inda ya zura kwallaye hamsin da tara a wasanni dari da tamanin da biyar da ya bugawa kulob din.