Ina cike da farin ciki- Guardiola

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pep Guardiola

Kocin Barcelona, Pep Guardiola, ya ce yana cike da farin ciki bayan da kulab din sa ya ci uku inda Real Madrid ta tashi da ci daya a wasan da suka buga ranar Asabar.

Real Madrid ce dai ta fara zura kwallo ta hannun Kareem Benzema, yayin da Barcelona ta yi wuf ta rama ta hannayen Alexis Sanchez, Xavi da kuma Cesc Fabregas.

Guardiola ya yabawa 'yan wasansa, yana mai cewa: ''Ban taba kaiwa irin wannan mataki ba, ba tare da wadannan 'yan wasa sun kokarta ba.Mun kokarta; kuma ina matukar farin ciki da yadda suka buga wasan''.

Ya kawar da yiwuwar cewa nasarar da suka samu za ta yi mummunan tasiri kan Real Madrid.

Ya ce: "Madrid za su mayar da jikinsu.Idan kana son ka ci irin wannan wasan dole ne ka jajirce, kuma mun jajirce.Amma duk da haka sune ke kan gaba, idan suka ci wasan da za su da Seville."