Za mu iya lashe gasar Premier - Villas-Boas

Villas-Boas Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Andre Villas-Boas ya jinjinawa 'yan wasan na Chelsea

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya ce za su shiga sahun wadanda za su iya lashe gasar Premier bayan da suka doke Manchester City a karon farko a Premier bana.

Fanaretin da Frank Lampard ya zira ana saura minti 8 a tashi ne ya baiwa Chelsea damar lashe wasan da ci 2-1a filin wasa na Stamford Bridge.

Kuma hakan ne ya kawo karshen wasanni 14 da City ta shafe ba tare da an yi nasara a kanta ba - kuma hakan ya rage tazarar da ta bayar a kan tebur zuwa maki biyu kacal.

A yanzu maki bakwai ne ya raba tsakanin Chelsea da Man City - kuma Villas-Boas na maida hankali wajen rage tazarar kafin karshen wannan shekara.

Ya ce: "Wannan babbar nasara ce kuma ta sauya matsayinmu wurin neman lashe gasar ta Premier. Tazarar maki bakwai ba wani abu bane, a wannan gasar ganin yadda kulob da dama ke fafutukar lashe gasar.

"Za mu ci gaba da kokari har zuwa karshen wasannin da za a gwabza a watan Disamba. Ina ganin ya kamata mu dora kan abinda muke yi yanzu".

Ya kara da cewa bayan matsalolin da muka fuskanta da farko, a yanzu mun farfado, kuma mun taka rawar gani a wasanmu da Man City.

Karin bayani