An doke Esperance a gasar zakarun duniya

Esperance Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Esperance ne zakarun Afrika na 2011

An doke zakarun kwallon Afrika Esperance a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na duniya a kasar Japan, inda suka zamo na karshe bayan Monterrey ta doke su da ci 3-2.

Esperance ne suka fara zira kwallo a minti na 31 ta hannun Yannick Ndjeng amma sai Monterrey wadanda 'yan kasar Mexico ne suka rama daga bisani.

Hiram Mier ne ya farke musu a minti na 39 kafin Aldo de Nigris ya zira kwallo ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan Jesus Zavala ya zira ta uku ne sai Khaled Mouelhi ya ci wa Esperance ta biyu daga bugun fanareti a minti na 75.

Kungiyoyin sun fafata ne bayan da Esperance ta sha kashi ranar Asabar a hannun Al-Sadd na kasar Qatar, yayin da ita kuma Monterrey ta sha kashi a hanun zakarun Japan Kashiwa Reysol.

Karin bayani