Man United na bukatar karin 'yan wasa - Ince

Vidic
Image caption Nemanja Vidic ba zai sake taka leda a kakar bana ba

Wajibi ne Manchester United ta sayi sabon dan wasan gaba da kuma wadanda za su maye gurbin Darren Fletcher da Vidic, a cewar tsohon dan wasan kulob din Paul Ince.

Dan wasan tsakiya Fletcher ya dauki hutu na sai hali yayi saboda rashin lafiya yayin da dan baya Vidic ba zai sake taka leda a kakar bana ba saboda raunin da ya samu a gwiwarsa.

Sai dai Ince na ganin suna bukatar karin dan wasan gaba domin ya taimakawa Wayne Rooney.

"Akwai matsin lamba da yawa a kan Rooney, kuma mun ga illar da hakan ya yi a kansa a lokacin gasar cin kofin duniya," kamar yadda Ince ya shaida wa BBC.

"Idan kana son fafatawa da irin su Manchester City da Chelsea kana bukatar dan wasan da zai iya zira kwallaye 20, kuma bai kamata a dogara kan Rooney ya rinka yin hakan duk shekara ba.

"Nani na haskakawa, haka kuma shi ma Ashley Young, sai dai sun dan yi sanyi, don haka ta ina kwallayen za su fito?

"Dimitar Berbatov ba ya taka leda yadda ya kamata, Michael Owen na fama da rauni, kuma har yanzu Danny Welbeck bai gama gogewa ba, amma zai iya taikama wa da wasu 'yan kwallaye."

Karin bayani