David Villa ya ji mummunan rauni

David Villa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan wasan kwallon kafa na Barcelona David Villa

Dan wasan kungiyar kallon kafa na Barcelona dan kasar Spain David Villa zai kwashe dogon lokaci baya taka leda sakamakon turgudewar daya samu a kafar sa.

Shi dai David Villa mai shekaru talatin ya ji rauni ne lokacin da yake taka leda a gasar cin kofin zakarun kullob kullob na duniya da Barcelona ta buga da kungiyar kwallon kafa ta Al Sadd na kasar Qatar.

Dan wasan da Barcelona ta saye shi daga Valencia kan kudi fam miliyan talatin da hudu a shekarar 2010, yaji rauni ne mintoci 39 da fara wasan, wanda Barcelona ta lashe da ci 4-0.

Villa wanda shine dan wasan da yafi cin kwallaye a kasar Spain inda ya ci kwallaye 50 a cikin wasanni 81, ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da Spain ta samu a gasar cin kwallon kafa ta duniya da aka fatata a kasar Afrika ta Kudu.

Sai dai wasu na ganin cewa mai yiwuwa raunin daya samu ka iya sa alamar tambaya game da kasancewar sa cikin jerin 'yan wasan kasar Spain da zasu fafata a gasar cin kofin kasashen turai a shekara mai zuwa.