Dede Ayew ne zakaran kwallon Afrika na BBC

Dede Ayew
Image caption Dede Ayew na karbar kyautar daga mahaifinsa Abedi Pele wanda ya lashe kyautar a 1991

An zabi dan wasan Ghana da Marseille Andre "Dede" Ayew a matsayin zakaran kwallon Afrika na BBC na shekara ta 2011.

Dan wasan mai shekaru 21 ya samu kashi daya bisa uku na kuri'un da aka kada inda ya bi sahun mahaifinsa, Abedi "Pele" Ayew, wanda ya lashe kyautar ta BBC a karon farko a 1991.

Ayew ya doke Yaya Toure, Gervinho, Samuel Eto'o da kuma Seydou Keita.

"Na yi murna da mamaki da lashe wannan babbar kyauta, musamman idan akai la'akari da manyan 'yan wasan da suka lashe a baya," a cewar Ayew.

"Nagode wa dukkanin mutanen da suka zabe ni - a Ghana, Afrika da ma sauran sassan duniya.

'Ba su yi zaben tumun-dare ba'

"Zan ci gaba da kokari sosai domin nuna musu cewa ba su yi zaben tumun-dare ba."

Masoya kwallon kafa na nahiyar Afrika ne suka kada kuri'ar ta hanyar email ko kuma sakon text.

Sun yi zaben ne daga jerin 'yan wasan da kwararru daga dukkan kasashen Afrika suka ware.

Bayan da ya taka rawa a fagen kasa-da-kasa a 2010 a gasar kasashen Afrika da kuma ta cin kofin duniya, Ayew ya ci gaba da haskakawa a fagen kulob.

Yana daya daga cikin 'yan wasan da ke taka leda kodayaushe a Marseille, inda ya zira kwallaye 11 a kakar 2010-2011.

A farkon kakar bana, ya taimakawa Marseille ta lashe gasar cin kofin French Super League - bayan da ya zira kwallaye uku.

Rauni ya hana shi taka leda a wasan farko da Marseille ta buga a gasar cin kofin zakarun Turai, amma ya buga kusan dukkannin ragowar wasannin.

Ya taka rawa a wasannin share fagen da Ghana ta buga na neman shiga gasar cin kofin kasashen Afrika.

Abedi "Pele" Ayew shi ne ya fara lashe kyautar zakaran kwallon Afrika na BBC a 1991.

"Dede" ya zamo dan kasar Ghana na biyar da ya lashe kyautar bayan mahaifinsa, Sammy Kuffour (2001), Michael Essien (2006) da kuma Asamoah Gyan da ya lashe a bara.

Wadanda suka taba lashe kyautar a baya

2010 - Asamoah Gyan (Sunderland & Ghana)

2009 - Didier Drogba (Chelsea & Ivory Coast)

2008 - Mohamed Aboutrika (Al Ahly & Egypt)

2007 - Emmanuel Adebayor (Arsenal & Togo)

2006 - Michael Essien (Chelsea & Ghana)

2005 - Mohamed Barakat (Al Ahly & Egypt)

2004 - Jay Jay Okocha (Bolton & Nigeria)

2003 - Jay Jay Okocha (Bolton & Nigeria)

2002 - El Hadji Diouf (Liverpool & Senegal)

2001 - Sammy Kuffour (Bayern Munich & Ghana)

2000 - Patrick Mboma (Parma & Cameroon)

Karin bayani