Zakarun Turai: Arsenal za ta kara da AC Milan

Kofin Champions League Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a buga wasannin farko a ranakun 14/15 ko 21/22 ga watan Fabreru

Arsenal za ta hadu da zakarun Italiya AC Milan a zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai, yayin da Chelsea za ta fafata da Napoli na kasar ta Italiya.

Arsenal da Chelsea, wadanda su ne suka rage a gasar daga Ingila, duka za su buga wasannin farko ne a Italiya.

Masu rike da kanbun Barcelona za su kara ne da Bayer Leverkusen na kasar Jamus.

Za a buga wasannin farko ne a ranakun 14/15 ko 21/22 ga watan Fabreru, yayin da za a yi wasanni na biyu a ranakun 6/7 ko 13/14 ga watan Maris.

Real Madrid, wacce ta lashe gasar sau tara, za ta fafata da CSKA Moscow na kasar Rasha yayin da Basel, wacce ta yi sanadiyyar korar Manchester United daga gasar, za ta hadu da Bayern Munich.

Inter Milan, wacce ta lashe gasar a shekara ta 2010, za ta hadu Marseille na kasar Faransa yayin da Lyon, za ta karbi bakuncin Apoel na kasar Cypuros wadanda ke halattar zagaye na biyun a karon farko.