Barca ta lashe gasar zakarun kulab na duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Barca yayin da suke daga kofin da suka lashe

Barcelona ta lashe gasar cin kofin zakarun kulab-kulab na duniya bayan da ta ci Santos hudu ba ko daya a wasan karshe da suka buga a Yokohama.

Hakan na nufin ta lashe kofuna uku kenan tun da dama ita ce zarakan kwallon Spain da Turai.

Lionel Messi ne ya fara zura kwallo, sannan daga bisani Xavi da Cesc Fabregas suka ci kwallo guda-guda kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Santos sun kokarta sosai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, amma duk da haka basu dace ba.

Messi ya zura kwallon karshe gab da za a kammala wasan.